WASHINGTON, D.C. - Magidantan biyu sun ba da labarin yadda suka sayar da kadarori, su ka ranto kuɗi, da kuma tara kuɗi daga dangi da masu hannu da shuni don ƙoƙarin tara kashin farko na dala miliyan biyu na fansa da Evans ya nema.
Mista Ahamonu, wanda aka daure hannuwansa da kafafunsa na tsawon watanni biyu da ya yi yana tsare, an sake shi ne a lokacin da iyalansa suka bai wa Evans kudin fansa dala 420,000, kuma a lokacin yana gab da mutuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa abokin Evans, Victor Aduba, wanda tsohon soja ne, shi ma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari kan wasu tuhume-tuhume hudu da suka shafi garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Da yake yanke hukunci, Oluwatoyin Taiwo, ya ce masu gabatar da kara sun yi nasarar tabbatar da shari’ar satar mutane da kuma mallakar bindigogi a kan wadanda aka yanke wa hukuncin.
Mutane da dama da ke zaune a yankin Festac da Amuwo Odofin a Legas sun koma Ikoyi da Lekki da Victoria Island inda suka bar gidajensu babu kowa saboda Evans.
Evans yana kuma da gungun masu garkuwa da mutane da suke gudanar da ayyukan sace mutane a Port Harcourt, Bayelsa da kuma Jihar Delta. Shi ne jagora kuma shi ne kadai wanda ya tsira daga yunkurin sace Cif Vincent Obianudo, mamallakin kamfanin Young Shall Grow Motors a Festac, Lagos a watan Agusta 2013.