Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Shugaba Buhari Ya Gayawa Dangin Fasinjojin Da 'Yan Ta'adda Su Ka Yi Garkuwa Da Su


Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wakilai da ‘yan’uwan mutanen da ‘yan ta’adda su ka yi garkuwa da su bayan sun fasa jirgin kasan da ke jigalarsu daga Abuja zuwa Kaduna watanni sama da hu’du da suka shige.

Wannan ne karon farko da Shugaba Buhari ya gana da dangin fasinjojin bayan da su ka shafe watanni suna jan hankalin gwamnati da ya hada da tattaki zuwa birnin tarayya Abuja inda suka rika gudanar da zangar zangar lumana da kuma zaman dirshe.

A yayin ganawarsa da dangin fasinjojin, Shugaba Buhari ya bayyana dalilan gwamnati na kin amfani da karfin soja domin kwato fasinjojin. Bisa ga cewarsa akwai yiyuwar asarar rayukan wadansu fasinjojin idan aka dauki matakin soja. Shugaban kasar ya bayyana cewa, akwai hatsari sosai wajen amfani da karfin soji idan ba ana da cikken tabbacin ratar da ke tsakanin maharan da wadanda su ke garkuwa da su ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su

Sai dai ya yi alkawarin yin dukan abinda aka iya wajen ceto sauran mutane 31 da har yanzu su ke hannun ‘yan ta’addan. Ya kuma yi alkawarin cewa, nan ba da dadewa ba za a sada su da danginsu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, an dauki matakai dabam dabam nan da nan bayan garkuwa da fasinjojin da nufin kwantar da hankalin dangin da kuma ganin hakan ba ta sake aukuwa ba a kasar.

A bayaninsa shugaba Buhari yace, Na sani cewa, a lokaci irin wannan hankali ya kan tashi,An ba mu shawarwari da dama game da amfani da karfin soji wajen kwato su. An yi nazarin wadannan shawarwari, sai dai an lura cewa, babu tabbacin za a iya ceto su ba tare da asarar rayukan wadansu daga cikinsu ba, dalili ke nan aka yi watsi da wannan shawarar, an ki ana so.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su

Shugaba Buhari ya kuma jajintawa wadanda su ka rasa danginsu a harin, da yace, tun lokacin da ‘yan ta’addan su ka kai hari ranar 28 ga watan Maris, 2022, al’ummar Najeriya baki daya suka shiga yanayin dimuwa da bakin ciki. Ya kuma bayyana cewa, babban aikin da ke gaban shi a halin yanzu shi ne na ganin an dawo da sauran mutanen an sada su da danginsu ba tare da ko kwarzane ba.

Dangane da umarnin da ya bayar kwanan nan ga jami’an tsaro na neman su kawo karshen cin zarafin bil’adama da basu ji ba, basu gani ba da ‘yan ta’addan ke yi, shugaba Buhari ya bayyana gamsuwa da ci gaban da ya ce jami’an tsaron suna samu, bisa la’akari da yawan ‘yan ta’addan da su ke kashewa a kwananin nan.

Yace, “Tilas ne mu yi farautar ‘yan ta’addan a inda su ke mu kuma nuna masu cewa, ba su da maboya a kasar mu. Za a yi farautar kowanne dayansu, a kuma dauki irin matakin da suka fi sani su ka kuma gwammace.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su

Tun farko a bayaninsa, Ministan harkokin sufuri Jaji Sambo, ya bayyana cewa, ya gana da dangin fasinjojin a makon farko da ya fara aiki a ma’aikatar, ya kuma bayyana masu kokarin da gwamnati ke yi na ceto danginsu.

Da yake maida martani, mai magana da yawun dangin fasinjojin, Alhaji Sabiu Mohammed, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta taimakawa wajen sako sauran fasinjojin da yar yanzu su ke hannun ‘yan ta’addan.

A kalla fasinjoji 970 ne ke cikin jirgin da ke kan hanyarshi zuwa Abuja daga Kaduna. Bisa ga bayanan shaidu, an kaiwa jirgin harin bom sau biyu kafin ‘yan ta’adddan da suka isa wurin kan Babura, su ka budewa fasinjojin wuta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dangin fasinhohin jirgin kasa 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su

Bisa ga bayanan shaidu, an kaiwa jirgin harin bom sau biyu kafin ‘yan ta’adddan da suka isa wurin kan Babura, su ka budewa fasinjojin wuta.

A kalla mutane 8 aka kashe a harin da su ka hada da shugaban matasa na jam’iyar APC mai mulki Amin Mahmoud, da wata likita Chinelo Megafu, da lauya Tibile Mosugu dan wani babban lauya a Najeriya, da kuma babban magatakardar Majalisar Kungiyar Cinikayya Barrista Musa Lawal.

Kawo yanzu, ‘yan ta’addan sun saki kusan mutane 50, yayinda su ke ci ga da garkuwa da sama da 30.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG