Wata kotun tarayya dake Abuja akarkashin mai shari’a Adeniyi Ademola yace ayi maza a rantsar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Adamawa Bala Bulus Ingilari a matsayin gwamnan jihar adamawa mai riko, mai shari’a Ademola yafadi hakane alokacin da yake yanke hukunci akan karar da tsohon mataimakin gwamnan ya shigar inda ya nemi a rantsar dashi akan matsayin Gwamnan mai riko har yagama wa’adin toshon Gwamnan jihar Adamawan Murtala Inyako, da aka tsige a ranar goma shabiyar ga watan bakwai na wannan shekara.
Festus Keyamu shine lauyan tsohon mataimakin Gwamnan Ingilari yace “Kundin tsarin mulki kashi dari uku da shida karamin sashe na daya zuwa biyar yaba mai shari’a Ademola hurumin yanke hukuncin wannan sashe yana bayanin cewa gwamnan jihar ne kadai keda hurimin ya karbi wasikar ajiye aiki da akace Igilari ya rubuta ba kakakin majalisa ba”.
Kuma gwamna Murtala inyako yayi rantsuwa cewar shi bai karbi takardar ajiye aiki a hannun Bulus Ingilari ba.
Kotu ta bukaci gwamnan jihar Adamawa me rikon kwarya na yanzu Ahmed Fintiri yayi maza-maza ya tara nasa da nasa yafita daga gidan gwamnati, sannan shugaban alkalan Adamawa ya rantsar da Bala Bulus Ingilari a matsayin gwamna mai riko batare da bata lokaci ba. Saikuma hukumar zabe data dakatar da zaben cika gurbi data shirya na ranar asabar goma ga watan nan da muke ciki.