Makonni uku bayan kama dolar Amurka miliyan tara da dubu dari uku a cikin jirgin saman shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya da hukumomin kasar Afirka ta Kudu suka yi, sai ga shi kuma, an kara kama wasu 'yan Najeriyar a kasar ta Afirka ta Kudu da wasu kudade dola miliyan biyar da dubu dari bakwai su ma kamar na farkon, na sayen makamai ne ta haramtacciyar hanya.
A kan wannan batu ne wakilin Sashen Hausa a shiyyar yammacin Najeriya Hassan Umaru Tambuwal ya tattauna da wani tsohon soja mai suna Mallam Dauda Dodo wanda ya ce gaskiya a irin tsarin da yayi aikin soja ba haka ake sayen makamai ba:
Jaridar City Press ta kasar Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa wadanda aka kama da kudaden sayen makamai suka je.