A yayin zaman nay au litinin, ‘yan majalisa 27 ne daga cikin 40 suka kada kuri’ar tsige Alhaji Abdullahi Yusuf Ata kuma suka maye gurbinsa da tsohon shugaban daya sauka a bara Hon Kabiru Alhassan Rurum wanda shine yanzu mataimakin shugaban majalisar.
A bara ne dai ‘yan majalisar suka matsawa lamba shugaba Rurum lallai ya sauka daga shugabancin majalisar ko kuma su tsige shi saboda zargin ya karbi naira miliyan 100 daga hannun hamshakin attajiri Aliko Dangote a matsayin toshiyar baki, domin majalisar ta dakatar da yunkurin ta na bincikar harkokin kudaden majalisar masarautar Kano a wancan lokaci.
Tun kasa da watanni 4 da suka shude ne ‘yan majalisar suka yi yunkurin tsige Hon Yusuf Abdullahi Ata saboda zargin sa da rashin shugabanci na gari, amma hakan ba ta faru ba, kawai sai abin ya tsaya akan mataimakin sa, kuma nan take aka zabi Alhassan Rurum ya karbi kujerar mataimakin shugaba.
Tuni dai sabon kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum ya sha alwashin daidaita al’amura dangane da tsarin shugaban ci a majalisar.
Koda yake ‘yan majalisar dokokin ba su alakanta matakin nasu na yau da batun sake shekar da tsohon gwamnan Kano ya yi zuwa PDP daga APC ba, amma masu kula da lamura na ganin cewa, matakin baya rasa nasaba da kakar zaben badi data fara kankama.
Batun yunkurin sauya shugabanci a majalisun dokokin na jihohi dana tarayya da kuma majalisar dattawa na ci gaba da daukar hankalin jama’a a fagen siyasar najeriya.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari
Facebook Forum