Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsayar Da Ranar Gudanar Da Sabon Zaben Kananan Hukumomi A Ribas


Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)

Hukumar zaben Ribas mai zaman kanta (RSIEC) ta tsayar da ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa domin gudanar da sabon zaben kananan hukumomi a jihar.

Kwamishinan zaben jihar, Mai Shari'a Adolphus Enebeli (mai ritaya) ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki daya gudana a yau Laraba, 5 ga watan maris din da muke ciki.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun koli ta zartar, wanda ya ayyana zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024, a matsayin wanda bai inganta ba.

Nigeria Politics Tinubu
Nigeria Politics Tinubu

A hukuncin da Mai Shari’a Jamilu Tukur ya zartar, kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda bai tabbata ba saboda mummunan saba dokar zabe da aka yi.

Da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Tukur yace ya ayyana matakin da hukumar zaben jihar Ribas ta dauka a matsayin wanda ba halastacce ba saboda rashin yin biyayya ga dokar zabe da sauran ka’idoji kasancewar ta ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a har bayan an sanar da ranar zabe.

Kotun ta kara da cewa an gaza bin tsare-tsaren gudanar da zaben kananan hukumomin inda karara hakan ya sabawa sashe na 150 na dokar zaben.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG