Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun kara tsawaita dokar ta baci a wasu yankunan kasar, zuwa wasu watanni 6 masu zuwa, bayan la’akari da yadda ‘yan ta’adda ke ci gaba da kai hare hare can da nan, matakin da Majalisar Dokoki ta yi na’am da shi bayan wata muhawarar da ta kai ga yin kuri’a a zauren majalisar a karshen mako.
Illahirin ‘yan majalisar da suka halarci wannan zama ne, suka kada kuri’ar amincewa bukatar ta gwamnati, wace ke ganin har yanzu akwai bukatar takaita zirga zirga da kai da kawo a yankunan Diffa, Tahoua, da Tilabery, wadanda tun a shekarar 2015 ke karkashin dokar ta baci sakamakon hare haren ta’addanci. Dan majalisar dokokin kasa na bangaren rinjaye, Alhaji Sama’ila Mai Aya, ya bayyana dalilansu na amincewa shawarar ta bangaren zartarwa.
Koda yake ba su yi wa gwamnati rowar kuri’arsu ba a wannan karo ‘yan adawa na zargin masu mulki da boye wata manufa a dangane da ainahin dalilan kafa wannan doka kamar yadda Karimou Boureima, daya daga cikin ‘yan majalisa daga mazabun yankin Tilabery, ya ce.
Sama da kashi 15 daga cikin 100 na kasafin kudaden kasa ne gwamnatin Jamhuriyar Nijer ke cewa ta na kashewa a ‘yan shekarun nan domin tunkarar kalubalen tsaro, sai dai ra’ayoyi sun sha bamban akan wannan ikirari.
A shekarar 2015 ne gwamnatin Nijer ta kafa dokar ta baci a yankunan Diffa, Tahoua, da Tilabery mai wa’adin watanni 6 kafin daga bisani a kara tsawaita wannan mataki bayan kowanne wata 6.
Ga cikakkaken rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum