An yankewa wata tsohuwar jami’ar bankin Najeriya hukumcin daurin watanni shida a gidan yari, bayan samunta da laifin aikata zamba,a shari’a irinta ta farko da aka yanke tun da aka fuskanci tabarbarcewar bankuna bara. Cecilia Ibru, daya daga cikin matan da suka yi fice a Najeriya, ita ce tsohuwar darektar bankin Oceanic. Jami’ai a kotun dake da zama a birnin Ikko sun ce, an yanke wannan hukumcin ne bisa yarjejeniyar amsa laifi da aka cimma da wadda ake tuhuma. Bisa ga cewar jami’an, Ibru, wadda iyalanta suka mallaki kamfanoni da dama a Najeriya, zata maida kaddarori da aka kiyasta kudinsu a kan dala miliyan dubu da dari biyu. Cecilia Ibru tana daga cikin manyan jami’an bankunan da gwamnati ta sauke daga mukamansu bara sakamakon tabarbarcewar bankunan kasar. Gwamnati tace bankunan sun kama hanyar durkushewa ne sabili da bada basusuka na fitar hankali aka rika yi da kuma rashin kyakkyawan shugabanci. Shekarar da ta gabata gwamnatin Najeriya ta zuba kimanin dala miliyan dubu hudu a bankuna tara dake neman durkushewa.
An yankewa wata tsohuwar jami’ar bankin Najeriya hukumcin daurin watanni shida a gidan yari.