Jami’an Tanzaniya na ci gaba da binciken cikin jirgin da ya nutse a kwana na uku, yayin da kuma aka fara gudanar da binciken yadda lamarin ya faru.
Tawagar masu bincike sun shafe yini guda suna ta ciro gawarwakin mutane daga cikin jirgin, wanda ya nitse sakamakon daukar jama’a fiye da ‘kima kamar yadda aka yi zargi, yayin da ake shiga kwana na hudu na makokin wadanda aka rasa.
Kamfanin dillancin labaru na AP ya fitar da rahoto jiya Asabar da ke cewa, an ceto mutum daya da rai. Haka kuma kafar labarai ta Wire Service na cewa an ceto wani injiniyan jirgin a kusa da injin jirgin, sai dai ba bayanin halin da yake ciki.
Baban sakataren gwamnatin Tanzaniya, John Kijazi, ya fadawa manema labarai cewa jirgin yana da adadin daukar fasinja 101 ne kacal. Kuma ya ce ya bayar da izinin a kaddamar da bincike, kuma za a tuhumi wandanda suke da hannu a hadarin.
Facebook Forum