Yau Talata ake cika shekaru 52 da hadin kan kasa- ranar da, a shekarar alib dubu da dari tara da sittin da hudu, Tanganyika ta hade da tsibirin Zanzibar suka kafa Tanzaniya.
Sai dai shugaban kasar John Magufuli mai ra’ayin garambawul, ya soke bukin ranar hadin kan kasa ta bana, a wani abinda ya bayyana a matsayin matakin rage barnar kudi. A maimakon haka, shugaban kasar ya bada shawara a yi amfani da kudin da za a kashe wajen gudanar da bukukuwan kan gyara hanyoyi.
Freeman Mbowe, shugaban jam’iyar adawa ta CHADEMA na kasa, yace hankalin al’ummar kasar a tashe yake sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a Zanzibar, da jam’iyar hamayya ta hakikanta cewa ita ta lashe
Bisa ga cewar Mbowe, soke bukin ranar hadin kan, ya nuna rashin iya sanin matakin da ya kamata a dauka na shawo kan rikicin siyasa da ake ciki a Zanbiri.