Wakilin Muryar Amurka ya tabbatar da cewa, jirgin Machar ya sauka a tashar kasa da kasa ta Juba yau Talata da rana, bayan jinkiri sama da mako guda, yayinda gwamnati da ‘yan tawaye suke jayayya kan abinda yarjejeniyar ta kunsa.
Za a rantsar da Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa, daga nan a fara daukar matakin kafa gwamnatin hadin kan kasa da shugaba Salva Kiir.
Sabani da aka samu tsakanin Kiir da Machar ya haddasa rikicin da kasar ta tsunduma ciki a watan Disamba shekara ta 2013. Fadan da aka shiga tun daga wancan lokacin, ya yi sanadin kashe dubun dubatan al’ummar Sudan ta kudu, yayin da sama da mutane miliyan biyu suka rasa matsugunansu.