Hukumomin Nijer sun bada sanarwar sassauta dokar hana fita da aka kafa a birnin Yamai, kusan tsawon akalla makonni hudu da nufin dakile yaduwar annobar cutar coronavirus.
Sai dai jama’a na ganin soke dokar kwata-kwata shine mafi a’ala, ganin yadda alkaluman baya-baya suka nuna cewa yawan wadanda suka harbu da kwayar cutar a kasar ya fara ja da baya.
A taron da ta yi a yammacin ranar laraba 22 ga watan Afrilu ne Majalisar ministocin kasar ta yanke shawarar sassauta wannan doka wacce ta hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, matakin da ya janyo mumunar zanga-zangar matasa a Yamai. Daga yau dokar za ta fara aiki daga karfe 9 na dare zuwa 5 na asuba.
Jami’in fafutika Hamidou Sidi Fody na kungiyar CODDAE, ya yaba da wannan matakin duk da yake ba haka aka so ba a cewarsa.
Kasancewar wannan sassaucin na zuwa ne a jajibirin watan azumin Ramadan dake matsayin wani lokacin yawaita ibada da sada zumunta a wajen musulmi, wasu mazauna birnin Yamai sun nuna rashin gamsuwa da sauye-sauyen da aka yi wa wannan doka.
Alkaluman hukumomin kiwon lafiyar al’ummar Nijer na cewa mutane 5 ne aka gano sun kamu da cutar coronavirus a iya binciken da aka gudanar a jiya laraba, yayin da a ranar Talatar da ta gabata bayanai suka nuna cewa mutum biyu kacal ne suka kamu da cutar, abinda ke nunin an fara samun saukin wannan annoba idan aka kwatanta da makonnin da suka gabata.
Ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar cewa mutane 662 ne suka kamu da cutar COVID-19 a Nijer yayin da wasu su 193 suka warke, sai dai mutane 22 sun mutu sanadiyar wannan annoba.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum