Yan rajin kare hakkokin bil Adama sun ce hare-haren da ake kaiwa ta jiragen sama a karkashin jagorancin Amurka sun fada kan wani mahimmin gari, a kan iyakar Syria da Turkiyya inda sojojin Kurdawa ke kokarin hana mayakan Daular Islama shiga.
Kungiyar lura da al'amuran hakkokin bil Adama a kasar Syria, mai cibiya a kasar Birtaniya, ta ce jiragen sama sun kaddamar da hare-hare biyar a kalla a yau Laraba a kudancin garin Kobani, wanda kuma ake kira Ayn Arab. Gumurzun da aka fafata a garin a 'yan makonnin baya ya sa mutane fiye da dubu 160 sun gudu sun nemi mafaka.
A makwafciyar kasar Iraki kuma, manyan jiragen saman yakin Birtaniya sun kaddamar da hare-hare a rana ta biyu kan mayakan kungiyar Daular Islama. Ma'aikatar tsaron kasar Birtaniya ta ce, sojojin gwamnatin kasar Iraki jiragen saman yakin ke tallafawa, kuma sun harba makamai masu linzami kan motocin 'yan tawayen a yammacin Baghadaza babban birnin kasar.
A halin da ake ciki kuma, Firai Ministan kasar Australia Tony Abbot ya ce manyan jiragen saman yakin sojojin kasar shi, za su yi aikin tallafawa kawancen kasashen da Amurka ke jagoranta, amma duk da haka, ya ce ba za su kai hare-hare su kadai ba tukuna.