Wata mata mai shekaru 30 ta rasu a Monrovia a makon da ya gabata, wato ‘yan wasu watanni bayan da aka ayyana kasar ta Liberia a matsayin wacce ta shawo kan cutar.
Mutuwar matar ta biyo bayan rasuwar wasu mutane hudu a Guinea da ke makwabtaka da kasar ta Liberia.
Mataimakin Ministan kiwon lafiyar Liberia, Tolbert Nyenswah, wanda shi ke kula da fannin yaki da cutar ta Ebola a Liberia, ya ce an sake samu bullar cutar ce daga Guinea da ke makwabtaka da su.
Sai dai ya ce ba kamar a baya ba, yanzu Liberia na da shirin da zai iya dakile bullar cutar a kowane lokaci.
A watan da ya gabata ne Guinea da ke makwabtaka da Liberia ta kara samun sabbin masu kamuwa da cutar, lamarin da ya sa Liberian ta yi maza-maza ta rufe kan iyakarta da kasar, tare da tura kwararru a fannin kiwon lafiya zuwa kan iyakokinta.