Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Shida Sun Rasu A Tagwayen Hare Hare Da Aka Kai A Mogadishu


Tagwayen hare hare a Mogadishu
Tagwayen hare hare a Mogadishu

A kalla mutane shida aka kashe da suka hada da maharan a wadansu tagwayen hare hare da aka kai yau asabar kusa da fadar shugaban kasar Somaliya dake Mogadishu, bisa ga cewar shaidu.

Shaidu sunce, wata mota dankare da nakiya a cikin gudu ta tarwatse wajen binciken ababan hawa kusa da wurin shakatawa da ake kira Peace Garden, daga nan aka yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindigan da jami’an tsaro.

Rahotannin farko na nuni da cewa, mutane shida da suka hada da sojan gwamnati da kuma mahara biyar aka kashe a harin.

An bayyana cewa, wadansu mutane sun ji rauni sakamakon hare haren.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG