Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Daya Daga Cikin Jagororin ‘Yan Adawa A Belarus.


Belarus Election
Belarus Election

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu da ba’a san ko su waye ba sun yi awon gaba da Maria Kolesnikova, Memba cikin jagororin ‘yan adawa a Belarus, a jiya Litinin a Mink,

Tuni kasashen Jamus da Birtaniya sun bukaci shugaban kasar ta Belarus Alexander Lukashenko da ya bayyana inda ta ke.

Ministan Harkokin Wajen kasar Jamus, Heiko Maas ya yi kira da a yi bayanin inda ta ke da kuma sakin dukkan fursinonin siyasa a Belerus,” a cikin wani jawabi da ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta wallafa a shafinta na twitter.

Shi ma a wani sakon Twitter da ya wallafa, ministan harkokin wajen Birtaniya, Dominic Raab ya ce akwai matukar damuwa sosai game da jin dadin Maria Kolesnikova a Belarus.

"Dole ne gwamnatin Lukashenko ta tabbatar da dawo ita gida lafiya. Wajibi ne kuma Gwamnatin ta tsagaita cin zarafi masu zanga-zanga, ta saki fursinonin siyasa da kuma fara zaman tataunawa tare ‘yan adawa."

Wata da ta shaidi yadda lamarin ya faru da aka bayyana da suna Anastasia, ta fadawa shafin yanar gizo na Tut.by Belarus a jiya Litinin cewa, ta ga wasu mutane da kayan farar hula sun tilastawa Maria shiga wata karamar bas kana suka tafi da ita.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG