Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Borno,Damian Chukwu, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa da yammacin Litinin, bayan wata zanga-zangar da 'yan a daidaita sahu ko kuma 'yan keke napep suka gudanar a birnin Maiduguri, inda suka rufe manyan titunan birnin, lamari da-ya kassara harkokin yau da kullum.
Masu aiki da keke-napep dai na zargin 'yan sandan da ke kula da zirga-zirgan ababen hawa wato Central Motor Traffic Division (CMTD) da karban na goro daga hannunsu ba bisa ka'ida ba a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan 'yan sanda ya bayyana cewa ana gudanar bincike akan wannan zargin.
"Idan muka samu sakamakon wannan bincike duk wanda muka samu da laifi za mu hukunta shi, ko shi wanene," inji kwamishinan.
Wasu masu keke napep sun bayyana dalilan da suka ya sa suka rufe manyan hanyoyin garin.
"Ma'aikata basu bari mu samu sukuni da zarar gari ya waye. Yanzu haka baburan mu da suka kama sun kai ashirin. Sun rike wai har sai mun zo da dubu daya da dari biyar, " in ji wani matukin.
Ya ci gaba da cewa sun sha kai kokensu ga manyan 'yan sandan amma basu yi komai ba a lokacin.
Wani kuma ya ce saboda yadda ake cin zarafinsu ne inda ake kai su dandal a rike su ba tare da sun aikata wani laifi ba.
Saurari cikakken rohoton Haruna Dauda
Facebook Forum