Darektar ta yi wannan kiran ne yayin kaddamar da taron karawa juna sani da Muryar Amurka ta shirya ga manema labarai dake shiyar Arewa maso gabashin Najeriya da aka gudanar a babban birnin Tarayya Abuja.
Uwargida Amanda Bennett ta bukaci manema labarai su yi amfani da kafofin sadarwarsu wajen kauda cutar da take katse hanzarin kananana yara ta kuma zama allakakai. Ta kuma ce gidan Radiyon Muryar Amurka zai ci gaba da aiki wajen ganin an kawar da wannan cuta daga doron kasa.
Mahalarta taron sun bayyana yadda taron ya kara masu karfin guiwar water da kan al’umma da kara zage dantse yayin gudanar da aikinsu da nufin ganin an cimma gurin shawo kan cutar baki daya.
Darektan Muryar Amurkan zata ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki uku tare da kai ziyarar kafofin watsa labarai, da kuma ganawa da jami’an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a harkar aikin jarida.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum