Wani kamfani mai suna SOGEMAZ da aka kafa ne zai kula da tafiyar da sabuwar kasuwar zamani Dole ta Damagaram.
Kimanin miliyan 500 ake bukata don fara aikin a wa'adi na shekaru 20 a matakin farko.
“Ya kamata a ce ‘yan kasuwa na jihar Damagaram, ya zamanto su ne masu karfin jari a wannan kasuwa, don saboda su yi iko da kasuwar, shi ya sa aka bas u kashi 50 na wannan kasuwa.” Inji
Alhaji Laminu Ammani, babban darekta na zauren ‘yan kasuwa a jihar ta Damagaram.
Ya kara da cewa tuni, har wasu ‘yan kasuwa sun fara zuba hannayen jari.
Musa Alhassan, Malami a Jami’ar Damagaram, ya ce wannan matakji zai bai wa ‘yan kasuwar damar samun wasu karin kudaden shiga a karshen shekara.
“Ko wanne dan kasuwa da ya kawo hannun jari a wannan kamfani da za a sa, ya zama kamar na su, duk matakin da za a dauka wajen kula da Kasuwar Dole da su za a yi, kenan idan aka ci riba a ko wacce shekara ko wanne dan kasuwa zai samu.” Alhassan ya ce.
Saurari rahoton Tamar Abari domin karin bayani:
Facebook Forum