Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Abdel Abdul-Mahdi A Matsayin Sabon Firai Ministan Iraqi


Barham Salih da Adel Abdul Mahdi
Barham Salih da Adel Abdul Mahdi

‘Yan sa’oi bayan zabenshi shugaban kasar Iraq, gogaggen dan siyasa Barham Salih ya zabi dan shi’a Abdel Abdul-Mahdi a matsayin Firai Minista, ya kuma umarce shi ya kafa sabuwar gwamnati.

An kebe matsayin shugaban kasa da ya kasance na jeka-na-yika, ga kabilar Kurdawa tunda aka fara gudanar da zabe mai jam’iyu da yawa a shekara ta dubu biyu da biyar, shekaru biyu bayanda Amurka ta jagoranci hambare gwamnatin shugaba Saddam Hussein.

Abdul-Mahdi wanda ya taba rike mukaman mataimakin shigana kasa, da ministan albarkatun mai da kuma ministan kudi, yana da kwanaki talatin ya kafa gwamnati ya kuma gabatar da sunayen ‘yan majalisa domin a amince da su.

Iraq dai ta gudanar da zaben majalisarta karon farko a watan Mayu, tunda aka murkushe kungiyar IS. Sai dai ba a sanar da sakamakon zaben ba, sai watan da ya gabata sabili da rigingimmun da suka barke dangane da sake kirga kuri’u.

Bayan an sake kirga kuri’un an tabbatar da cewa, jam’iyar babban malamin ‘yan shi’a Muqtada al-Sadr ce ta sami kuri’u mafiya yawa, ya kuma lashe kujeru hamsin da hudu cikin kujerun majalisa dari uku da ishirin da tara. Sai hadakar kungiyar da ta hada kan kungiyoyin mayakan ‘yan Shia tazo ta biyu da kujeru arba’in da bakwai, sai kuma hadakar kungiyar PM Haider al-Abadi tana biye da kujeru arba’in da biyu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG