Bincike ya nuna cewa zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Bauchi bai gudana ba kamar yadda aka shirya.
Wannan lamarin ya sa ‘yan takara guda uku suka kaddamar da taron manema labarai inda suka bayyana matsayinsu. Wadanda suka kira taron su ne Farfesa Ali Pate, Dr Yakubu Ibrahim Lame.
Farfesa Pate y ace sun kira taron ne domin su yiwa al’ummar jihar Bauchi bayani. Zaben da aka shirya za’a yi ba’a yi ba. Babu wani zabe dake gudana. A wuraren da jama’a suka taru su yi zabe, wani wurin babu kayan zaben, Wani kuma babu ma masu shirya zaben A karamar hukumar Bogoro tashin hankali ma aka yi har wani ya rasa ransa. Farfesa Pate y ace a cikin garin Bauchi a saka wa mutane barkonon tsohuwa an kuma dakesu.
Yace sun yi kokarin su tabbatar an yi zabe mai adalci amma hakkansu bai cimma ruwa ba. Saboda haka su ukun nan sun sha alwashin ba za su ake shiga zaben ba sai an dakatar da shuwagabbin jam’iyyar na jihar.
Amma a wasu wurare zaben wadanda suka isa wurin sun shaidawa Sashen Hausa cewa sojoji ko ‘yan sanda ne suna ta jefa maso barkonon tsohuwa kana ana jifan iyayensu ‘yan fansho da duwatsu. Sun ce zabe kam a Bauchi ba’a yi ba. Wata ta ce an baza su an fada masu babu maganar zabe. Tana cewa an yi masu rashin adalci saboda an watsa masu barkonon, an tarwatsa su kamar ‘yan awakai.
A wani wurin kuma wani cewa ya yi tun karfe 10 suke tsaye suna jiran a kawo kayan zabe amma shiro kamar an shuka dusa baicin jami’an tsaro da suke wurin.
Amma zaben fidda da dan takara na jam’iyyar PDP ya gudana inda tsohon ministan Birnin tarayya Bala Muhammad ya yi nasara. Haka ma a jihar Gome inda jam’iyyar APC ta zabi Alhaji Inuwa Yahaya a matsayin gwaninta. Haka kuma ita ma PDP ta tsayar da Sanata Usman Bayero Nafada.
A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad
Facebook Forum