Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kwace Lasisin Gidan Rediyon Acik Dake Birnin Istanbul


Priministan Turkiyya Reccep Erdogan.
Priministan Turkiyya Reccep Erdogan.

Hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai na Radio da Talbijin ta Kasar Turkiyya RTUK ta kwace lasisin wata tashar Radio mai zaman kanta a ranar Laraba, sakamakon barin baki game da kisan kiyashin da aka yi a Armenia, a tashar.

Matakin na RTUK na kwace lasisin tashar Acik Radio mai mazauni a Istanbul, wadda ta fara yada shirye shiryen ta a shekarar 1995, ya biyo bayan wani bako da aka gayyato a ranar 24 ga watan Apirilu, wanda yayi wata baram barama akan kisan kiyashin Armenia.

Bakon da aka yi hira da shi a tashar yayi baram baramar ne inda yace, a bana an haramta bikin tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar Armeniya

Ranar 24 ga Afirilu ta kasance wata rana ta tuna yakin duniya na daya, lokacin da daular Ottoman, wanda ya gadar da Turkiyyar wannan zamanin ta kashe dubbun dubatan Armeniyawa. A shekarar 2021 ne, a karon farko, Shugaban Amurka Joe Biden, ya amince da ranar 24 ga watan Afirilu, a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa Armaniyawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG