Shugabar hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Filato, Madam Julie Bala, ta ce akwai ‘yan gudun hijira fiye da 38,000 daga sassa daban-daban na jihar da ke bukatar taimako da tsaro don komawa gidajensu.
Madam Julie ta bayyana hakan ne, yayin da kungiyar 'yan jarida ta jihar ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira da ke Haipang a karamar hukumar Barkin Ladi, inda ta tallafa musu da kayayyakin abinci, tufafi da sauransu.
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta ware mako guda a matsayin makon 'yan jarida.
Mai Magana da yawun ‘yan gudun hijirar, Iliya Makam wanda ya yaba da ziyarar ta ‘yan jaridar ya gabatar da bukatunsu na magunguna da abinci musamman saboda masu fama da cutar sukari.
Wata 'yar gudun hijira, Binta Bello, ta ce suna bukatar abinci da abin kwanciya.
A daya bangaren kuma, shugaban kungiyar ta 'yan jarida, Mr. Paul Jatau ya ce labaran bogi, sau da dama su ke haddasa tashin hankali ba ma a Najeriya kadai ba har da wasu kasashen duniya.
Jihar Filato ta sha fama da rikice-rikice da ke da nasaba da addini da kabilanci, inda daruruwan mutane suka mata kana aka yi asarar dumbin dukiyoyi.
Facebook Forum