Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi anfani da lafazi mai gauni wajen la’antar mummunan farmakin ta’addancin da aka kai ran Asabar din da ta gabata a kan wani barikin sojan Majalisar Dinkin Duniya dake arewancin kasar Mali.
An kashe akalla soja daya na rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a lokacin wannan harin da aka kai akan barikin dake Timbuktu, kuma an raunana mutane da dama, ciki harda sojoji bakwai na Faransa.
Rundunar sojan Faransa tace maharan sun nuna kwarewa sosai wajen shirya kai farmakin, wanda ya hada da shigar burtun da suka yi na sanya kayan sojan Majalisar Dinkin Duniya na rundunar da ake kira MINUSMA.
Har zuwa yanzu dai ba wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai harin, koda yake an san cewa akwai kungiyoyi masu matsancin ra’ayi da dama dake zaune a yankin da abin ya faru.
Facebook Forum