Kungiyar da take zama a Birtaniya mai sa ido a kan take hakkin bil adama a Syria ta Syrian Observatory, ta ce farmakin ya auna kauyen Zardana dake arewa maso yammacin gundumar Idlib.
Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wurin, ya ce tarin mutanen da suka ji rauni da ake kulawa dasu a asibitocin yankin, sun hada ne da mata da kananan yara da tsofaffi da kuma ma’aikatan ceto.
Sai dai an kawana biyu ba’a sami irin wannan farmaki ta sama a kan garin na Idlib ba a cikin yan watannin da suka gabata.
Dubun dubatar mutane da suka rasa matsugunansu daga wurare a cikin kasar ta Syria, yanzu suna zaune ne a Idlib.
Facebook Forum