Hukumomi a kasar Malawi sun hana jana’izar bai daya ga mutane 7 da aka hallaka a lokacin zanga-zangar da aka yi a garin Mzuzu na arewacin kasar.
Masu makoki sun hallara a harabar dakin ajiye gawan da gawarwakin mutane 7 din ke ciki, inda su ka zake cewa sai sun gudanar da bison bai daya din duk ko da fargabar da hukumomi ke yi cewa hakan ka iya kara tayar da fitina.
Sojoji sun yi ta sintiri a garin Mzuzu da sauran manyan birane a yau Jumma’a, bayan da mutane 18 su ka hallaka a wata zanga-zangar kin gwamnati a farko wannan satin.
Mummunar zanga-zanga ta barke jiya shekaran jiya Laraba a birane uku mafiya girma a kasar wato Mzuzu da Blantyre da kuma babban birnin kasar wato Lilongwe sanadiyyar tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin take ‘yancin dan adam.
Shaidu sun ce ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu boren da ke wasoson kayan wasu shaguna. Irin salon murkushe zanga-zangar ya janyo suka daga Amurka, da Burtaniya da Majalisar Dinkin Duniya.
A jiya Alhamis, Shugaba Bingu wa Mutharika ya yi jawabi ga kasar ta gidan rediyo, inda ya yi kiran da a kwantar da hankula ya kuma ce a shirye ya ke ya tattauna da masu adawa da shi.