‘Ya’yan jam’iyyar PDP, mai mulki a jihar Gombe, sun bayyana rashin jin dadin su a bisa kalaman da Gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo, yayi , a dagane da halin matsi da jama'ar jihar suke fama dashi.
Shi dai Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bayyana cewa halin kunci da kuma na zafin aljuhu da mutanen jihar ke fuskanta a halin yanzu ya biyo bayan salon zaben 2015, da jama’ar suka yi ne da suka tsaya a linta maimakon su kai rufin kwano.
Da yake maida martani akan batun da gwamnan yayi, wani jigo a jam’iyyar PDP, a jihar Gombe Alhaji Garba a koma gona, yace maganar ta Gwamnan da mammaki domin kuwa mutane jihar Gombe, sun nuna masa halarci.
Yace ‘yan jam’iyyar PDP, a jihar Gombe, abinda suka fahimta da wannan Magana shine, cewa Gwamna Dankwambo, yana jin haushen faduwar tsohon shugaba Goodluck Jonathan.
Yakara da cewa idan dai biyan bukata ne na zabe mutanen jihar Gombe sun nuna masa kauna domin sun dawo dashi kan mulki, kuma babu hujjar da Dankwambo ke dashi da zai yiwa mutanen Gombe gori.