Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kasa Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Kan Tsibirin Cyprus


Wani dan kasar Cyprus dauke da kwalin mai rubutun nuna kishin kasa
Wani dan kasar Cyprus dauke da kwalin mai rubutun nuna kishin kasa

An kawo karshen zaman tattaunawar da ake a kasar Switzerland kan tsibirin Cyprus ba tare da cimma wata matsaya ba.

Wani zaman tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Switzerland don kokarin kawo karshen cijewar da ta kawo rabuwa a tsibirin Cyprus har na tsawon sama da shekaru 40, ya zo karshe ba tare da an kulla wata yarjejeniya ba.

A yau Juma’a ne babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce “Abin mamaki, yarjeniya ba za ta yi tasiri ba, kuma an rufe taron ba tare da cimma burin warware dadaddiyar matsalar ba.”

Mutanen da suka sami halartar taron na samar da masalaha kan tsibirin sun hada da jami’an Girka da shugabannin Turkiyya da kuma Birtaniya.

Manyan jami’an kungiyar tarayyar Turai ma sun halarci taron.

Cyprus dai ta kasance a rabe tun 1974, lokacin da dakarun Turkiyya suka mamaye daga baya kuma suka kwace Arewacin, a wani yunkurin mayar da martanin samun karuwar goyon bayan hada kai da Girka.

Turkiyyar ta ajiye dakatunta 35,000 a arewacin Cyprus. Hakan ya sa Girkawa ke kallon lamarin a matsayin barazana suka kuma gargade su da kwashe nasu-ya-nasu su fice daga yankin.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya ce babban muradin zaman tattanawar na Switzerland shine Girka da Cyprus na neman Turkiyya ta kwashe sojojinta daga tsibirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG