Jirgin karshen da ya sauka a filin tashi da jiragen sama na Yarima Bin Abdulaziz dake madina dauke da ragowar alhazai daga jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Bauchi, Abuja da kuma jihar Neja, jimilla su 211, ana kuma sa ran kamfanoni masu zaman kansu zasu kammala kwashe maniyatan su kafin rufe filayen jirgin sama na saudiyya.
A wata sanarwa da ta fito daga hannun jami’ar yada labaran hukumar NAHCON Hajiya Fatima Sanda Usara ta bayyana cewa a ranar 22 ga wannan watan bayan kammala aikin hajji hukumar zata fara dawo da alhazan Najeriya.
Shugaban ofishin kula da harkokin alhazai dake Madina, Alhaji Ibrahim Idris Mahmud, ya ja hankalin maniyata game da bin dokokin kasar Saudiyya inda ya jaddada muhimmancin katin sheda na maniyata da kasar Saudiyya ta fito dashi domin dakile masu kutse cikin alhazai.
Ya kuma bayyana cewa hukumar Saudiyya ta sanar dasu cewa duk wanda aka kamashi bada kati ko shaidar gudanar da aikin hajji ba, hukuncin shine biyan tara Riyal 10,000 tare da mai dashi kasar sa kuma sai bayan shekara 10 kafin ya kara shiga kasar Saudiyya.
Game da lafiyar alhazai kuma tawagar likitocin Najeriya ta sha damarar wayar da kan alhazai kan daukar matakan kaucewa zafin rana daka iya haifar da matsalar matsanancin zafi ko 'heat stroke' a turance da ka iya barazana ga rayuwar su da kuma jaddada muhimmancin shan ruwa inji jagoran tawagar likitocin dake kula da alhazan Dr. Abubakar Adamu Ismail.
Shugaban Izala (JIBWIS) na Najeriya Sheik Abdullahi Bala Lau ya bawa alhazan shawar ne dasu gudanar da aiyukan su na ibada kamar yadda addinin Islama ya karantar.
Duk da cewa wannan shine ya zama mafi tsadar kujerar hajji a tarihi wasu daga cikin alhazan sun bayyana ra’ayinsu da samun wannan dama, inda suka yaba da dukkan ayyuka da tsare-tsare na hajjin bana.
Saurari rahoton Hauwa Umar:
Dandalin Mu Tattauna