Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da damke wadansu ‘yan bindiga tara da ke ikirarin aiki a matsayin mayakan sa-kai na “CIVILIAN JTF” a garin Arufu da ke kan iyakar jihohin Benue da Taraba, wadanda biyar daga cikin su ke dauke da bindigogin AK 47 shake da albarusai.
Nan take, wasu sunyi kokarin hana sojoji tafiya da su sheldkwatar bataliyar soji, sai dai yunkurin nasu ya gamu da cikas.
Kwamandan bataliyar, Laftanar kanar Ibrahim Gambari yayi wa manema labarai karin haske dangane da lamarin inda yace jami’an tsaro ba zasu amince da kungiyoyin banga ba, domin gudun tsunduma cikin wani rikici ganin irin matsalolin da ake fuskanta da suka hada da satar mutane domin kudin fansa, satar shanu, kisan dauki-dai dai da fashi da makami.
Wadansu sun zargi gwamnatin jihar Benue da daukar nauyin ‘yan JTF din da samar mu su makamai, zargin da gwamnatin jihar ta musanta.
Ga Cikakken rahoton da Wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul’ziz ya aiko daga Yola, jihar Adamawa:
Facebook Forum