Rundunar ‘yan sanda ta jihar Binuwai ta tabbatar da cewa an kashe jami’anta biyu a wani kwantan bauna da aka yi musu a yankin karamar hukumar Logo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Moses Yamu, yace an tura jami’an ‘yan sandan ne zuwa yankin domin shawo kan rikicin da ake yi. Ya bayyana cewa, an kama mutane takwas makon da ya gabata biyo bayan rikicin, an kuma gurfanar dasu gaban kotu. Yace gwamnatin tarayya tana daukar mataki domin kwantar da hankalin jama’a dake zaune a cikin yanayin tsoro musamman a kan iyakar jihar da Nassarawa.
Sakataren agajin gaggawa na jihar Binuwai, Emanuel Shior yace akwai akalla ‘yan gudun hijira na cikin gida sama da dubu takwas dake zaune a sansanoni biyar a kananan hukumomi biyu da rikicin ya shafa, yayinda kuma sama da ‘yan gudun hijira dubu goma daga kudancin kasar Kamaru suka sami mafaka a Karamar Hukumar Kwande.
Ga Cikakken rahoton da Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji ta aiko daga Jos:
Facebook Forum