Majalisar Dinkin Duniya na shirin aikawa da karin sojojin kiyaye lafiya zuwa yankin na Abyei bayanda wani kazamin fada day a kaure a wurin ya laume rayukkan mutane akalla 70.
Kan hakan ne Majalisar Dinkin Duniya tace zata kwaso sojoji kamar 100 daga wassu sassa na Sidan, ta aika su can yankin na Abyei inda akace mata da yara kanana na ci gaba da arcewa don ceton kansu.
Fadan ance ana tapka shi ne tsakanin mayakan Misseriya dake tareda hukumomin arewancin Sudan da kuma na ‘yan kabilar Ngok Dinka dake tareda da kudancin Sudan.
Da jami'an gwamnatin Kudanci da Arewacin Sudan na zargin juna da mara wa wani bangare a rikicin. Sojojin bangarorin biyu sun ki amincewa da zargin kasancewa da hannu a rikicin.
Haka zalika a jiya Alhamis, Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai bukatar warware rikin Abyei a siyasance cikin gaggawa.