Jiya Talata aka fara sauraran ‘karar da jihar Oklahoma dake nan kasar Amurka ta shigar kan kamfanin hada magunguna Johnson & Jonshon, bisa rawar da kamfanin yake takawa a barkewar annobar kwayar ipioid a Amurka.
Wannan itace shari’a ta farko irinta da aka taba yi, wadda ta zargi wani kamfanin hada magunguna da alhakin matsalolin ta’ammali da miyagun kwayoyi, wanda zai iya shafar sauran jihohi dake da irin wannan fushin.
Da yake gabatar da jawabin bude shari’ar lauyan Jihar Oklahoma Mike Hunter, ya Kira barkewar annobar kwayar opioid da cewa “mummunar matsala ce da ‘dan Adam ya samar ga lafiyar al’umma a tarihin jihar da ma kasar baki daya.”
Hunter ya kwatanta matsayin kamfanin Johnson & Johnson da cewa kudi ya rufe masa ido yana yaudara tare da cutar da mutane.
Facebook Forum