Saudi Arebiya ta ce an “matukar lalata” mata wasu jiragen ruwa na dakon man fetur a wani “hari da aka kai “da gangan” a jiya Lahadi a kusa da gabar tekun kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sai dai Har yanzu, babu wani karin bayani, kan yanayin barnar da aka yi wa jiragen.
Ministan makamashin Masarautar ta Saudiyya, ya ce, daya daga cikin jiragen dakon man, ya na kan hanyarsa ta zuwa tashar jirgin ruwan kasar mai suna Ras Tanura don dauko man fetur ya kai Amurka.
Da sanyin safiyar yau Litinin, Amurka ta fitar da wani gargadi kan abin da ta kira “hare-hare da aka kai da gangan” wadanda suka auna wasu jiragen ruwan da ke gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara ta-da jijiyar wuya tsakanin Amurka da Iran.
Tunda farko, kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce a jiya Lahadi, an hari wasu jiragen ruwan kasuwanci guda hudu da nufin “a hana su yin zirga –zirga” a kusa da yankunan ruwanta a Gabar Tekun Oman.
Sai dai amma ba su ba da wani cikakken bayani ba kan irin barnar da wadannan hare-hare suka yi, wadanda aka kai su da gangan, sai dai kawai ta ce, jiragen sun fito ne daga kasashe daban-daban.
Facebook Forum