Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Firai Ministan Isra'ila


Israel Palestinians
Israel Palestinians

An gaggauta ficewa da Prime Ministan Isra’ila Benjamen Netanyahu a dandalin jawabai, a wani gangamin yakin neman zabe a birnin gabar teku na Ashkelon da ke kudancin kasar ta Isra’ila, bayan da aka harba wata roka daga Zirin Gaza da yammacin jiya Laraba.

Na’urar garkuwa daga manyan makamai ta tare roka daya da aka harbo daga Gaza, a cewar rundunar sojin Isra’ila.

An kai Netanyahu da matar sa Sara a wata maboya da ke kusa a yayin da rokar ta ke kara. Daga bisani ya koma domin iyar da jawabin sa a gangamin.

Shugaban na Isra’ila yana yakin neman zabe ne gabanin zaben fitar da gwani a yau Alhamis, inda zai fafata da dadadden abokin adawar sa Gideon Saar, a shugabancin jam’iyyar Likud.

Haka kuma yana fuskantar babban zabe na 3, shekara daya bayan sakamakon zaben watannin Afrilu da Satumba, sun nuna zai sake gwabzawa da Benny Gantz, a yayin da cikin su ba wanda ya sami isassun kuri’un da zai kafa gwamnati.

A watan da ya gabata, an tuhumi Netanyahu da laifin zamba, cin hanci da cin amanar kasa a kararraki 3 daban-daban. To amma ya jaddada musanta dukkan zarge-zargen.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG