Colvin ta mutu ne tare da wani dan jaridar daukar hoto Bafaranshe Remi Ochlik, lokacin da gwamnatin Bashar al-Assad ta yi dabarar harba makanin roka zuwa wani matsugunin ‘yan jaridu a birnin Homs da ke gundumar Bab Amr a ranar 12 ga Fabrairun 2012.
Har wasu ‘yan jarida 3 ma sun jikkata a wajen. Wata kungiyar rajin kare ‘yan jaridu a birnin New York tace, gwamantin Syria ta kashe su ne saboda kar su tona asirin kanshin mutuwar da aka yi aka kashe mutane a Homs.
Ministan yada labaran kasar Syria yace, a lokacin da abin ya faru, gwamnatin ba ta ma san Colvin da Ochlik suna kasar ba.
An dai shigar da wannan karar ne a madadin ‘yar uwar Marie da ake kira Cathleen Colvin da sauran iyalansu a shekaran jiya Asabar, a babbar kotun Amurka da ke nan birnin Washington DC.