Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Janye Dokar Ta Baci A Kasar Turkiyya


An janye dokar ta-bacin da aka sanya a kasar Turkiyya biyo bayan yunkurin yiwa shugaba Rajib Tayip Erduwan, juyin mulki da bai samu nasara ba a shekarar 2016.

Matakin janye dokar wadda ta fara aiki da safiyar yau Alhamis, na zaman wani alkawari da shugaba Erduwan, ya dauka a lokacin da aka sake zaben shi a matsayin shugaban kasa cikin watan da ya gabata.

An kulle mutane fiye da dubu 75,000 a karkashin dokar ta-bacin haka kuma an kori ma’aikata sama da dubu 100,000 daga ayyukan gwamnati, bisa zargin sun yi alaka da mabiyan wani malamin Turkiyya, Fetullah Gulen, da ke zama kasar Amurka, wanda Turkiyya ta dorawa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, da kuma kungiyoyin mayakan kurdawa.

‘Yan majalisar kasar Turkiyya, sun fara muhawara akan wasu dokoki yau Alhamis da zasu ba hukumomi damar cigaba da korar ma’aikatan gwamnati har na tsawon shekaru 3, da hana gudanar da tarurruka da maraice, haka kuma hukumomin su sami damar rike mutanen da suke zargin suna da hannu a batun har na tsawon kwanaki 12 ba tare da an tuhume su da wani laifi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG