Matasan da aka zabo daga kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa an horas da su ne kan yadda zasu samar da bayanai ga jami’an tsaro, da tabbatar da bin doka da kan tituna da duba gari masu tabbatar da tsabtar gari da kuma malaman daji da zasu takaita yadda ake sarar itatuwa don hana kwararowar hamada.
Kwamandan hukumar kare al’umma ta Civil Defense a jihar Nasarawa, Mohmmad Gidado Fari, ya ce sun horas da matasan ne kan samun bayanan tsaro a tsakanin al’umma, kan yadda zasu kare kansu daga hadari da yadda zasu kula da kansu a cikin taron jama’a da kuma makatan da za su bi wajen kama mai laifi.
Wasu daga cikin matasan da suka sami horon sun nuna karfin gwiwarsu wajen yin aiki da abin da aka koyar da su wajen samar da ci gaba ga al’umma.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum