Sanin kowa ne sana’ar canjin kudin kasashen waje na daya daga hada-hadar da jama’a suka yiwa kamun kazar kuku a Najeriya. Ta inda kafin kaga mutane sun je banki neman canjin kudi sai ya zama ba yadda zasu yi, don suna ganin ya fi riba.
Kwatsam sai ga sanarwa ta fito daga babban bankin Najeriya na CBN cewa, duk wani dan canjin kudin da bas hi da rijista da gwamnati, wannan sana’a ta haramta gare shi. Tsarin da babban bankin ke ganin yana cikin yunkurin ceton darajar Naira.
Baya ga ‘yan canji masu rijista, akwai dubban mutane da ke reto a ofisoshi da shagunan ‘yan canji suna wannan harkar, hasali ma dai it ace babbar sana’ar da suke ci suke sha kamar yadda wani dan canji ya bayyanawa wakilinmu Lamido Abubakar Sakkwato.
Ga dukkan alamu ‘yan canjin bas u yi maraba da wannan garambawul na CBN ba, domin a ganinsu suna saukakawa mutane wajen samun canjin kudin waje ba tare da wahala ba.
Sai dai shima mai magana da yawun babban bankin Ibrahim Mu’azu ya fayyace wadanda ake nufi da wannan doka. Inda yace akwai halattacciya da kuma haramtacciyar hanyar yin wannan sana’a ta canjin kudi.