Baya ga hayakin kuma warin da kamfanonin ke janyowa al'umma su dai wadannan cututuka da gurbatar muhalli ke haddasa su sannu, a hankali su ke shiga cikin jkin mutum, su taru su kuma kawo ila ga lafiyarsa.
Wani likitan al'uma da ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dr Usman Bashir, yayi bayani akan ilolin muhali ga lafiyar bil'adama da irin cututukar da mutum ke iya dauka.
Dr Bashir yace, "Hayakin da suke tasowa na girke-girke, na janareto, na motoci, wanda suke gurbata muhali, sukan kawo cututuka dayawa, ko kuma su tsananta wasu cututuka, kamar cutar Asma."
Ya kuma ce, "Wadansu cututukan sukan shiga jini suyi illa."
Dr Bashir ya bukaci mutane su kare kansu daga shakan wadanan hayaki da kuma zuwan asibiti domin a duba lafiyar su da zarar sun fuskanci wani canji a lafiyar jikinsu.
Ga cikakken rahoton da Barak Bashir ta aiko.