Dr. Gajere yayi wannan kiran ne a tattaunawa da ‘yan jaridu, a lokacin ganawa ta biyu a yunkurin yaki da tarin fuka a kananan hukumomi 23 na jihar.
Gajere yace akwai wurare 168 na bada magani da kuma dakunan bincike 63 a cikin jihar, ya kara da cewa shirin ya dauki masu wayar da kan al’umma akan cutar. Bisa ga cewarshi, cutar fuka tana da muni da kuma hadarin gaske saboda yadda take yaduwa cikin sauri kasancewa iska take yada ta ko’ina. Dr. Gajere kuma ya shawarci mutane suje duba kansu duk lokacin da suka kamu da tarin da ya wuce sati biyu. Yace gwajin, duba lafiya da yin magani ga tarin fuka kyauta ne, kuma ya gargadi ‘yan Nigeriya su yi amfani da wannan damar domin su san lafiyarsu.
Daya daga cikin masu gudanar da irin wannan binciken a jihar ya bayyana cewa, kalubalai da ake fuskanta a aiwatar da shirin sun hada da rashin kyaun hanyoyi da kuma rashin sa kai tsakanin al’umma na neman sanin ko suna dauke da cutar.