Matsalar ta fara ne a sati biyu da suka wuce, ta kashe yara biyar ya zuwa yanzu.
Yawan majiyata da aka nemarwa magani a asibitin Gordinia ya karu zuwa 450, shugabannin lafiya a yankin sunce wannan ce matsalar kiwon lafiya mafi muni da aka samu cikin shekaru 30.
Dr Mark Atkins, likitan wannan yankin yace, suna kokarin sanin dalilin wannan cutar. Ya bayyana cewa yara da yawa na zuwa asibiti domin jinya magani, kuma ana yi masu jinya bisa abinda aka gani cikin bincike. Banda jinyar wadanda suka kamu da cutar, ana kuma yin bincike domin gano abinda ya kawo wannan cutar.
Duk da haka, ya shawarci iyaye su yi sauri domin neman magani, idan suka ga alamun yara na kashi mai yawa. Ya kuma shawarci iyaye su rika ba yara ruwa sosai, ya gargadi mazauna wannan yanki su nemi hanyoyin kiyaye yaduwar cutar.