Shugaban shirin na kasa, Mr. Pius Sunday ne ya bayyana haka a cikin wata hira ga manema labarai a wata ziyara da ya kai birnin Kebbi.
Bisa ga cewarshi, za a samar da dakunan bincike 15 karkashin shirin, inda za’a ajiye magunguna a kuma rika jinyar wadanda suke fama da cutar.
Mr. Pius Sunday ya bayyana cewa, za a rika yiwa masu fama da cututukan jinya kyauta. Kuma tuni aka jihar magungunan ciwon tarin fuka.
Shugaban yaki da cutar ya gargadi masu fama da cutar su rika zuwa domin shan magani domin maganin ciwon da yace yana da muni da ake iya warkarwa.
Mutane 400 ne yanzu suke shan magani a dakunan shan magani dabam dabam na jihar.