Da yake magana kan shirin, babban likita mai kula da shirin allurar rikafi a jihar ta Naija, Dr. Yabage Aliyu, yace Sashen ya kammala dukkan shirye shirye na ganin an sami nasarar shirin wanda zai dauki kwanaki hudu.
Dr. Yabage, yace, tuni suka kammala horas da wadatattun ma'aikata da zasu tafiyar da wannan aiki, kuma har an tanadi da magungunan da ake bukata saboda shirin.
A karshen shirin na kwanaki hudu ana sa ran yara sama da milyan hudu ne za'a yiwa allurar rigakafin.
Sai dai, kungiyar wadanda suke fama larurin nakasa sakamakon kamuwa da cutar shan-inna, ta koka kan ci gaba da tswangwama da 'yan kungiyar suke fuskanta daga sauran jama'a.
Shugaban kungiyar reshen jihar Naija, Mallam Awwal Ahmed, yace idan suka tafi a wasu hukumomi, idan za'a rubuta sana'arsu, ba'a ma tambayarsu, sai kawai a rubuta cewa ai su mabarata ne.
Ga karin bayani.