Sa’ao’I kafin fara zaben, gwamnati ta bada umarni ga kamfanonin dake bada layukan internet da su rufe shafukar yanar gizon gidajen jaridu da na yada labarai 15, ciki har da Muryar Amurka da Radio Free Asia da kuma jaridar Phnom Penn Post
Phos Sovann shine babban jami’I mai kula da bayanai da watsa labarai a ma’aikatar yada labarai ta kasar, ya tabbatar da wannan labarin, kana Muryar Amurka ta samu wannan bayani a rubuce a wata takarda da ta samu daga ma’aikatar yada labaran.
Rusa babbar jami’iyar adawa ta Cambodian National Rescue Party da kotun kolin kasar ta yi a bara, yasa ana kyautata zaton firayi ministan kasar Hun Sen kuma dan takararr Cambodian People’s Party mai mulki ne zai lashe zaben.
Jami’iyar ta lashe zabuka a baya, wanda ke bata wa’adin shekaru biyar biyar. Shi kuma Hun Sen ya dere kan mulkin kasar kimanin shekaru 30.
Facebook Forum