Duk kuwa da cewa an hangi fuskokin su a wurin liyafar bankwana da shugaba Buharin ya shiryawa ministocin da suke neman takara a matakai daban daban.
Kwana guda bayan umarnin sauka daga mukamai ga wadanda ke da muradin tsayawa zabe a cikin ministocin nasa ranar larabar da ta gabata, shugaba Buhari ya kuma shirya musu liyafar bakwana a fadarsa dake Abuja.
Ko da yake ministan shari’a Abubakar Malami da takwaran na kwadago Chris Ngige sun halarci liyafar, wadda hakan ke nuna cewa, sun shiga jerin masu tsayawa zabe, amma daga bisani ministocin biyu sun sanar da jayewar daga neman takara.
Wannan mataki ya haifar da ayoyin tambaya game da makomar mukaman su, inda ‘yan Najeriya, musamman masana dokokin kasa da masharhanta a fagen demokaradiyya ke tafka mahawara.
Femi Falana mai lambar aikin lauya ta SAN na mai ra’ayin cewa, tunda ministocin biyu sun fita daga ofis tilas ne sai shugaba Buhari ya sake mika sunayen su ga majalisar dattawa domin tantancewa, kafin su iya komawa bakin aiki, yana mai kafa hujja da sashi na 306 na kundin mulkin kasa.
Hakan dai na kara nanata muhimmancin bukatar fadar shugaban kasa ta fayyace al’amura domin ‘yan kasa su sami waraka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: