Wani furucin da yayi a farkon makon nan, Jakadan Amurka Johnnie Carson yace Amurka ta nuna matukar damuwar matakin da hukumomin Nigeria suka dauka n adage lokacin zaben tun da farko. Yace hakan da hukumomin Nigeria suka yi ka iya kauda amincewar da ‘yan Nigeria keyi da sahihancin shugabanninsu dake cewa sun shirya tsaf wajen karfafa salon mulkin Dimokuradiyya a kasar. Kuma hakan na iya tabbatar da zargin cewar hukumomin Nigeria ba zasu iya kaucewa irin magudin zaben da ya afku a zaben shekara ta 2007 ba.
A halin da ake ciki, hukumar zaben Nigeria, ta sake jaddada cewar za’a gudanar da zaben majalisar dokokin Nigeria ran Asabar kamar yadda aka tsara amma ba za’a iya kauda tsammanin sake dage ranar zaben ba.A tattaunawar da yayi da manema labarai Alhamis, shugaban hukumar zaben Nigeria Farfesa Attahiru Jega yace za’a gudanar dazaben a dukkan mazabun ‘yan majalisardattawa 109, im banda wasu mazu 15. Sannan ba za’a gudanar da zaben a mazabun ‘yan majalisar wakilai na tarayyar Nigeria 46 ba.