Tun bayan samun bullar cutar coronavirus a Najeriya, wasu ‘yan kasa da ma kungiyoyi masu zaman kansu ke mika gudunmawar su domin yaki da cutar.
Fadar gwamnatin kasar ta ce an samu zunzurutun Naira miliyan 776.
Bayan da aka fara samun korafe-korafe akan yadda ake aiwatar da kudaden, Hukumar Yaki da Cin Hanci ICPC ta ce, za ta fara bincike akan lamarin.
A wata sanarwa da ke dauke da sa hanun Shugaban ayyuka na hukumar ICPC Akeem Lawal, ya bayyana cewa hukumar ta fara bincike akan zarge-zargen al’mundahana da wasu bangarorin hukumomin Gwamnati suka yi wajen rabon tallafin, da zargin rashawa wajen sayo kayan tallafin da kudaden zirga-zirga, da kudaden da aka kashe wajen wayar da kan al'umma a game da cutar.
Lawal ya ce, akwai jihohi da suke binciken yadda gwamnatoci suka tatsi kananan hukumomi da sunan annobar, sannan akwai kuma inda aka karkatar da kudaden tallafi.
Daya cikin Shugabanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke da hadin gwiwa da hukumar ICPC wajen binciken, Halima Baba Ahmed ta ce, duk wanda aka kama da hannu a cikin badakalar, komai girmansa za a gurfanar da shi a gaban Kuliya.
Ta kuma yi kira ga al'umma da su yi hakuri su baiwa Hukumar ICPC hadin kai a wajen ba da bayanai, don hana rashawa da almundahana kamar yadda dokokin kasa suka tanadar, tare da bin umurnin shugaban kasa wajen tabbatar an yi gaskiya wajen kashe kudaden.
Kwararre a fanin zamantakewar dan Adam kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum, Mohammed Ishaq Usman ya ce, bayan fara irin wannan binciken akan dauki lokaci mai tsawo ana yi. Amma ya ce daga baya akan shagaltar da al'amarin.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.
Facebook Forum