Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fyade: ‘Yan Majalisun Najeriya Na Neman Warware Matsalar A Kasar


Majalisun Najeriya sun bukaci a sanya ‘yan sanda mata sashin bincike kan yiwa yara fyade domin samun mafita.

A yayin da matsalolin da suka shafi cin zarrafin mata wadanda suka hada da yiwa yara mata da maza har ma da manyan mata fyade ke karuwa a kwanakin baya-bayan nan, yan Majalisun Tarayyar Najeriya da gwamnonin jihohi da kuma masu fafutukar kare yara sun bukaci a sanya yan sanda mata a sashin bincike kan fyade.

Haka kuma sun nemi a wayar da kan iyaye su tashi tsaye, su daina rufawa masu aikata fyade baya, lamarin da ke kara sa wadannan miyagu ke ci gaba da aikata ta’asar.

Ita ma ministar harkokin mata, Pauline Tallen ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta bada umarnin tabbatar da cewa an kawo karshen wannan lamarin, inda ta mika bukatar a kafa kotuna na ko-ta-kwana domin hukunta duk wanda ya aikata fyade nan take.

Duk da kiraye-kirayen da masu fafutukar kare yara ke yi saboda matsalolin fyade na baya-bayan nan, lamarin dai na karuwa inda ake zargin wani dan shekarar 25 da yiwa wata dattijuwa mai shekara 70 fyade a jihar Ogun, batun da ya jawo muhawara a Majalisun Tarayyar Najeriya, inda yan Majalisu suka mika bukatar a fara yanke hukuncin mai tsanani a kan duk wanda aka kama da laifin fyade.

Dan majalisar wakilai, Dr. Shehu Wamban Koko, mai wakiltar mazabar Koko na jihar Kebbi, a tarayyar Najeriya ya bayyana cewa, rashin bincike a bangaren ‘yan sanda ke tsananta lamarin.

A wani bangare kuwa, gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, cewa ya yi sai al’umma sun farga tare da hada karfi da karfe domin kawo karshen lamarin saboda a kare mutuncin ‘ya’ya mata.

A ranar Alhamis ne dai yan Majalisar Wakilan Najeriya suka yi watsi da kudurin neman a daddage duk wanda ya yiwa yarinya karama fyade da James Faleke, mai wakiltar mazabar Ikeja na jihar Legas a tarayyar Najeriya ya gabatar, inda wasu ‘yan majalisa suka amince a koma yin amfani da gundarin dokar daurin rai da rai.

Kazalika, yan Majalisar Dokokin jihar Osun ma sun amince da daurin rai da rai ga duk wanda ya aikata fyade kuma duk wanda ya yi yunkurin yi, zai shafe shekara 14 a kurkuku.

Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdurah’uf.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG