Wakilin Muryar Amurka ya shiga garin Tilabery daga mashigar garin na bangaren gabas zuwa yamma yau ranar da aka fara amfani da babura a dukan sassan jihar bayan haramcin shekaru a kalla 3 da aka yi, inda ya yi hira da wasu mazaunan garin da suka bayyana farin cikinsu da janye dokar da suka ce ta tauye hanyoyin samun abin zaman gari.
Tsawon lokacin da aka dauka na hana aiki da injina sakamakon yadda sha’anin tsaro ke ci gaba da lalacewa a yankin Tilabery ya sa wasu mutane dangana da babura, yayinda wasu daga cikinsu suka sayar wasun kuma sun boye abinsu a gida.
Kafin zuwan wannan rana hukumomi sun yi rajistar sunayen mutanen da suka mallaki babura tare da daukan lambobin kowane machine danganin komai ya gudana cikin tsari kuma.
A hirar shi da Muryar Amurka, mataimakin magajin garin Tilabery, Assabir Mounkaila, ya bayyana cewa, an sanar da jama’a cewa za a iya hawan babur ne daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma.
To amma wani matashi Mahamadou Oumarou na da damuwa game da sharuddan da aka gindayawa mamallaka babura.
Yace wannan mataki na rajiastar babura ya na da matsala a wajensu domin an baka takarda dauke da sunanka da hotonka don ka fara amfani da machine dinka to amma kuma idan wani zai yi aro ko ka bashi haya ba zai yiyu ba.
A shekarar 2017 ne gwamnatin jamhuriyar Nijer ta kafa dokar ta baci a jihohin dake fama da matsalar tsaro cikinsu har da jihar Tilabery. Tsanantar yanayin tsaro ya sa aka haramta amfani da babura a wannan yanki mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso.
Korafe korafe a game da yadda dokar ta kawo koma baya a harkokin yau da kullum ya sa mahukunta sassauta wannan doka a bisa sharadin amfani da babura da rana a matsayin matakin gwaji na tsawon watanni 2 daga yau laraba 1 ga watan satumba.
Saurari cikaken rahoton cikin sauti: